Amurka

Pelosi ta gabatar da kudurin bada damar bincikar lafiyar shugaban Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump yayin gaisawa da shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi
Shugaban Amurka Donald Trump yayin gaisawa da shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi Win McNamee / Getty Images

Shugabar majalisar wakilan Amurka ‘yar jam’iyyar Democrat Nancy Pelosi, ta gabatar da kudurin wata dokar gyara ga kundin tsarin mulkin kasar, wadda za ta baiwa ‘yan majalisar damar bincikar ko shugaban kasa na da cikakkiyar lafiyar jagoranci ko kuma akasin haka, abinda zai bada damar mikawa mataimakinsa ragamar shugabanci.

Talla

Kudurin Pelosi na zuwa ne yayinda ake ci gaba da diga ayar tambaya kan halin da shugaban Amurka Donald Trump ke ciki bayan kamuwa da cutar coronavirus.

Sai dai yayin ganawa da manema labarai, shugabar majalisar wakilan Amurkan, ta musanta cewar kudurin na da alaka da halin da Trump ke ciki.

Pelosi dai ta yi kaurin suna wajen caccakar Trump bisa banbancin ra'ayi ka manufofi da dama, abinda ya sanya a Disambar shekarar 2019 ta jagoranci yunkurin tsige shugaban na Amurka.

Tuni dai shugaba Trump ya bayyana cewa sam babu abin fargaba game da komawarsa White House daga Asibiti, inda ya ce yana jin kwarin jiki fiye da yadda ya ke ji shekaru 20 da suka gabata.

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter Trump ya ce ko kadan kada jama’a su razana da Covid, kar su bari fargabar cutar ta tauye rayuwarsu.

Zuwa yanzu Amurkawa miliyan 7 da dubu dari 4 suka kamu da cutar ta Covid-19 ciki har da dubu 210 da cutar ta kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.