Armenia da Azerbaijan na zargin junansu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Wani sashin yankin Nagorno-Karabakh da yaki ya rusa.
Wani sashin yankin Nagorno-Karabakh da yaki ya rusa. BULENT KILIC / AFP

Armenia da Azerbaijan sun zargi junan su da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma kan yakin da suka kwashe akalla makwanni 2 suna gwabzawa kan mallakar yankin Nagorno-Karabakh.

Talla

Takaddamar ta baya bayan nan ta haifar da shakku kan dorewar yarjejeniyar sulhun wucin gadin da aka cimma tsakanin kasashen 2 a karkashin jagorancin kasar Rasha.

Makasudin yarjejeniyar tsagaita wutar dai shi ne bada damar musayar fursunonin yaki tsakanin kasashen na Armenia da Azerbaijan.

Tattaunawar da ta gudana tsakanin bangarorin biyu a birnin Moscow ita ce ta farko, bayan barkewar yaki kan yankin Nagorno-Karabakh.

A hukumance dai yankin bangare ne na kasar Azerbaijan, sai dai mafi akasarin al’ummarsa ‘yan Armenia ne, kuma su ke shugabantarsa.

Daruruwan mutane ciki har da sojoji daga dukkanin kasashen suka rasa rayukansu a yakin na makwanni 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.