Jamus-Poland

COVID-19: Jamus da Poland sun sake takaita walwalar jama'a

Wasu mata sanye da takunkuman rufe baki da hanci tare da wasu ma'aikatan lafiyar kasar Poland a Warsaw, babban birnin kasar. 8/10/2020
Wasu mata sanye da takunkuman rufe baki da hanci tare da wasu ma'aikatan lafiyar kasar Poland a Warsaw, babban birnin kasar. 8/10/2020 © Czarek Sokolowski / AP

Jamus da Poland sun kafa sabbin dokokin yaki da annobar coronavirus, wadda a yanzu haka ke cigaba da yaduwa a kasashen da kuma sauran sassan Turai bayan sake barkewa a karo na biyu.

Talla

A Berlin babban birnin Jamus, za a rika rufe wuraren shan barasa da gidajen abinci daga karfe 11 na dare sabanin kwana da suke yi a bude, daga yanzu har zuwa 31 ga watan Oktoban da muke, yayinda ita kuma Poland ta banbanta lokacin da tsofaffi da matasa ke ziyartar kasuwanni.

Tuni dai shugabar gwamnatin Jamus ta baiwa yankunan da ke fuskantar sake barkewar annobar coronavirus wa’adin kwanaki 10 da su dakile cutar, ko kuma ta bada umarnin sake killace mutane a gidajensu.

Tsaurara matakan da Jamus gami da Poland suka yi, na zuwa ne yayinda a nahiyar kasashen latin da yankin Carribean yawan mutanen da suka kamu da cutar ya zarta miliyan 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI