Faransa: An gano karin mutane kusan dubu 27 da suka kamu da coronavirus
Wallafawa ranar:
Adadin mutanen da ke kamuwa da cutar coronavirus a Faransa na ci gaba da hauhawa, duk da kokarin hukumomin kasar na dakile annobar da ta sake barkewa a karo na 2.
Alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar a baya bayan nan, sun nuna cewar mutane dubu 26 da 896 aka gano sun kamu da cutar ranar asabar kadai a Faransar, adadin da ba a taba gani ba tun bayan da annobar ta bulla cikin kasar a farkon wannan shekara.
Tuni dai hukumomin kasar suka sake maido da dokokin takaita walwalar jama’a, ciki har da rufe gidajen abinci da na shan barasa, a wasu manyan biranen da suka hada da Paris, Marseille, Lyon, da Saint-Etienne.
A halin yanzu jumillar adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Faransa ya kai dubu 718, da 873, ciki har da dubu 32 da 684 da annobar ta kashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu