Birtaniya

Akwai yiwuwar sake kulle Birtaniya baki daya

Firaministan Birtaniya Boris Johson zai gabatar da shirinsa na tsauraran matakan yaki da corona ga Majalisar Dokokin Kasar a yau Litinin.
Firaministan Birtaniya Boris Johson zai gabatar da shirinsa na tsauraran matakan yaki da corona ga Majalisar Dokokin Kasar a yau Litinin. Jeremy Selwyn / POOL / AFP

Fitaccen masanin kimiya a Birtaaniya Farfesa Peter Horby, ya bayyana cewa, akwai yiwuwar sake kulle kasar baki daya saboda annobar coronavirus, amma ya ce za su yi tsayin-daka don ganin hakan bai tabbata ba.

Talla

Farfesa Horby ya ce, Birtaniya ta shiga wani yanayi mai hatsari a daidai lokacin da adadin masu fama da Covid-19 da kuwa wadanda ake kwantarwa a asibiti ke ci gaba karuwa.

Kalaman Farfesan sun karfafa wadanda Mataimakin Babban Jami’in Lafiyar Kasar ya yi, inda ya ce, za a samu karin mamata, yana mai gargadin jama’a da su rika nesa nesa da juna.

A yau Litinin ake sa ran Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai sanar da tsauraran matakan yaki da cutar coronavirus, inda zai aika wasika ga Majalisar Dokokin Kasar, wadda a cikinta zai fayyace shirinsa na yaki da cutar a matakai uku, inda kowanne yanki na Ingila zai kasance karkashin tsarin da ya fi dacewa da shi, ma’ana dai za a yi la’akari da tsananin cutar a kowanne yanki.

Mista Johnson ya kwashe tsawon yinin jiya Lahadi yana shaida wa Majalisar Ministocinsa matakan da zai dauka.

Sai dai tuni shirin nasa ya fara shan suka daga bangaren ‘yan adawa, inda ‘yan majalisun kasar daga jam’iyar Labour a Greater Manchester, suka shaida masa cewa, ba za su goyi bayan kafa tsauraran matakai ba.

Ko a jiya Lahadi dai, sai da mutane fiye da dubu 12 suka harbu da kwayar cutar ta coronavirus a Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI