EU ta gargadi Turkiya kan ci gaba da aikin hakar gas a Mediterranean
Wallafawa ranar:
Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi Turkiya kan matakin na sake aikewa da jiragen binciken iskar gas gabashin Tekun Mediterranean a kokarinta na ci gaba da aikin hakar gas, matakin da kungiyar ta bayyana a kokarin tayar da hankula.
Tun a lahadin da ta gabata, Turkiya ta sanar da shirin komawa aikin laluben iskar ta gas a gabashin tekun Meditrerranean yayinda a jiya Litinin jiragenta da suka faro aikin a watan Agusta suka koma gabashin tekun don ci gaba da aiki.
Sai dai babban jami’in Diflomasiyya EU Jopsep Borrell ya bayyana matakin na Turkiya da kokarin dawo da rikici la’akari da yadda kasahe 3 ke takaddama kan mallakar yankin, yayinda ya sanar da shirin tattaunawa kan batun a taron EU da zai gudana cikin makon nan.
Kasashen Girka da Turkiya dukkaninmsu mamabobin kungiyar tsaro ta NATO sun fada rikici ne bayan gano tarin albarkatun iskar gas makare a yankin na gabashin Medeterranean wanda dukkanninsu ke ikirarin mallakarsa.
Gabanin dakatar da aikin hakar iskar ta gas ta Turkiya ke yi a farkon watan nan, EU ta gargade ta kan yiwuwar fuskantar takunkumai matukar ta ci gaba da aikin wanda ke shirin haddasa yamutsu bayan da tun a wancan lokaci kasashen biyu ta kai su ga girke jiragen yaki a iyakarsu ta ruwa.
A zantawar Josep Borrell da manema labarai a Luxembourg bayan kammala taron ministocin wajen kasashen EU ya ce matakin na Turkiya abin takaici ne domin kuwa zai kara rura wutar rikicin yankin maimakon taimakawa wajen yayyafa masa ruwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu