Turai-EU

EU ta tsawaita tallafa wa kamfanonin Turai

Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen
Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen Yves Herman/Reuters

Hukumar Tarayyar Turai ta sanar da shirinta na tsawaita bada tallafi ga kamfanonin cikin gida domin habbaka tattalin arzikin kasashenta da coronavirus ta kassara. Hukumar ta ce, wannan shirin zai ci gaba da aiki har zuwa tsakiyar shekarar 2021.

Talla

A farkon wannan shekarar ce, Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai ta sassauta tsauraran matakan tallafa wa kamfanoni da zummar bunkasa bangaren tattalin arziki da ya samu nakasu sakamakon annobar Covid-19 wadda ta girgiza duniya.

Da farko dai hukumar ta ce, sassaucin zai kawo karshe ne a ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa, amma za a ci gaba da bada tallafin har zuwa badi.

A cikin sanarwar da ta fitar a birnin Brussels, hukumar ta EU ta ce, ta dauki matakin ci gaba da bada tallafin ne ganin yadda har yanzu harkokin hada-hadar kasuwanci ke cikin bukatar tallafi.

Kazalika hukumar ta gabatar da wani sabon mataki domin bai wa kasashe mambobinta damar agaza wa kamfanoninsu da ke tafka asara.

Sama da mutane dubu 241 suka mutu a sanadiyar cutar coronavirus a nahiyar Turai kadai, yayin da ta harbi miliyan 6.5 a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI