Faransa

Tsanantar Coronovirus a Faransa zai tilasta sake kulle kasar

Firaministan Faransa, Jean Castex ya yi gargadin cewa zai zame wa hukumomi tilas su sake rufe kasar a kokarin dakile bullar annobar Coronavirus da ta sake kunno kai kuma ta ke kokarin cin karfin asibitoci.

Firaministan Faransa Jean Castex.
Firaministan Faransa Jean Castex. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

A wata ganawa da gidan rediyon France Interenationale, Castex ya ce idan a cikin makonni biyu masu zuwa annobar ta ta’azzara, ta inda sashen masu bukatar kulawa ta musamman ya cika ya batse fiye da yadda aka yi tsammani, daukar karin matakai zai zama wajibi.

Da aka tambaye shi a game da sabbin dokokin zama a gida da rufe wuraren sana’o’i, firmanistan ya ce komai na iya faruwa duba da irin abubuwan da suke gani a asibitoci a halin yanzu.

Castex ya jaddada cewa kamata ya yi a kaucewa rufe ilahirin kasar kamar yadda aka yi na tsawon watanni biyu a yayin da cutar ta kai kololuwa, amma matsalar ita ce mutane da dama sun kasa fahimtar cewa cutar ta sake dawowa, inda ya ce a halin da ake ciki, jihohin Toulouse da Montpellier, na cikin shirin ko ta kwana ya zuwa daren Lahadi, abin da ya kai adadin jihohin da abin ya sake shafa 9.

A karshen makon da ya gabata, ma’aikatar lafiyar Faransa ta sanar cewa mutane dubu 27 ne suka harbu da wannan cuta a ranar Asabar, ranar Lahadi ta sanar da fiye da mutane dubu 16, da kuma jimillar dubu 32 da dari 7 da 30 da suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI