Asibitocin Paris sun tumbatsa da masu corona
Hukumomin Faransa sun ce asibitocin birnin Paris na gaf da cika, ganin yadda marasa lafiyar da ke fama da cutar coronavirus suka mamaye kashi 90 na gadajen da ake da su.
Wallafawa ranar:
Shugaban Hukumar Kula da Asibitocin birnin ya bukaci a kara zage dantse dangane da shirin tarbar wata sabuwar ambaliyar masu fama da annobar wadda ta sake kunno kai a karo na biyu.
Mista Martin Hirsch da ke shugabntar asibitoci 39 na birnin Paris ya ce ba za a iya kauce wa faruwar ambaliyar mutanen da suka kamu da cutar ta Covid 19 ba a kasar musaman a birnin Paris.
A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an gano akalla mutane 800 zuwa dubu 1 da suka kamu da cutar ta Covid 19, alkalumman da ke nuna cewa, an samu karin marasa lafiyar da kimanin kashi 70 zuwa 90 cikin 100 a birnin na Paris kadai.
Wannan dai ya kara jefa shugaba Emmanuel Macron cikin halin tsaka mai wuya, yayin da ake sa ran zai bayyana ga al’ummar kasar a wata tattaunawa ta talabijin da za a watsa a maraicen wannan Larabar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu