Faransa-Covid

Macron ya sa dokar hana yawon dare a birane 8 bayan karuwar masu Covid-19

Shugaba Emmanuel Macron yayin jawabin kai tsaye ta gidan Talabijin.
Shugaba Emmanuel Macron yayin jawabin kai tsaye ta gidan Talabijin. France 2

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanya dokar hana fitar dare a birnin Paris da kuma wasu birane 8 sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar Covid-19.

Talla

Yayin amsa tambayoyin manema labarai ta kafar talabijin, shugaban yace mazauna wadannan birane zasu dinga shiga gidajen su daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safe daga ranar asabar mai zuwa na tsawon makwanni 4.

Macron yace daukar matakin ya zama wajibi domin dakile yadda cutar ke yaduwa, yayin da yace matakin zai hana mutane zuwa gidajen abinci da kuma gidajen jama’a cikin dare.

Garuruwan da dokar ta shafa bayan birninParis sun hada da Grenoble da Lille da Lyon da Marseille da Montpellier da Rouen da Saint-Etiene da kuma Tolouse.

Shugaban yace duk wanda aka samu ya karya dokar zai fuskanci tarar euro 135 ko kuma Dala 159.

Shugaban yace kasar na cikin yanayin damuwa, duk da kokarin da hukumomi keyina shawo kan annobar, amma duk da haka ba za’a killace mutane a gida kamar yadda akayi na watanni 2 a baya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI