Babu abin da zai hana Masuntan Faransa kamun kifi a ruwan Birtaniya- Macron
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sake jaddada matsayin sa na cewar masunta kasar sa ba za su daina zuwa yankin Birtaniya suna kamun kifi ba, yayin da ya halarci taron shugabannin kungiyar kasashen Turai da ke gudana a Brussels.
Batun kulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kungiyar kasashen Turai da Birtaniya da ta fice daga cikin ta na daga cikin manyan batutuwan da shugabannin ke tattaunawa a wajen taron, ganin yadda aka samu tsaiko da kuma rashin daidaito daga bangarorin biyu.
Shugaba Emmanuel Macron ya ce koda sunan wasa, masuntan Faransa ba za su sadaukar da halarcin da suke da shi na kamun kifi a ruwan Birtaniya ba, domin kuwa basu suka bukaci ficewar kasar daga Turai ba.
Macron ya ce bai wa masuntan kasar damar kamun kifi a ruwan Birtaniya na daga cikin sharuddan da ya zama dole a amince da su a tataunawar da ake.
Shugaban na Faransa na daga cikin wadanda suka dauki matsayi mai karfi dangane da batun kamun kifin a cikin watanni 6, saboda ganin an bai wa masunta kasashen Turai damar kutsa kai inda su ke so domin gudanar da sana’ar su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu