Harin makamai masu linzami ya halaka fararen hula 12 a Azerbaijan
Gwamnatin Azerbaijan ta ce fararen hula 12 sun rasa rayukansu a wani farmaki da dakarun Armenia suka kai mata da makamai masu mai linzami a yau asabar, wanda ya rusa gwamman gidaje a Ganja, birni na biyu mafi girma a kasar, lamarin da ya haifar da jikkatar wasu fararen hular da dama.
Wallafawa ranar:
Farmakin na baya bayan nan dai na nuna yadda yakin da aka shafe kusan makwanni 3 ana gwabzawa kan mallakar yankin Nagorno-Karabakh ke kazanta tsakanin kasar ta Azerbaijan da makwafciyarta Armenia.
Rahotanni sun ce farmakin makamai masu linzamin kan Azerbaijan ya biyo bayan makamancin harin da dakarun kasar suka kaiwa na Armenia a birnin Stepanakert, babban birnin yankin na Nagorno Karabakh da Armeniyawa suka fi rinjaye cikinsa.
Sake barkewar yaki tsakanin kasashen dai ya rusa kokarin masu shiga tsakani da ya kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin 2, lamarin da ya haifar da fargaba kan yiwuwar janyo Rasha dake marawa Armenia baya da kuma Turkiya mai goyon bayan Azerbaijan cikin rikicin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu