Faransa

An kama karin mutane 5 kan yankan ragon da aka yiwa malami a Paris

Wasu jami'an 'yan sandan Faransa
Wasu jami'an 'yan sandan Faransa ABDULMONAM EASSA / AFP

Hukumomin Faransa sun kama karin mutane 5 baya ga wasu 4 da ke tsare, da a ke zargin suna da hannu a kisan da wani mutum ya yiwa malamin makaranta ta hanyar yankan rago ranar Juma’a a birnin Paris.

Talla

Tuni dai Jami’an tsaron na Faransa suka bindige mutumin har lahira.

Bayanai sun ce mutumin da bincike ya nuna cewar matashi ne mai shekaru 18 dan asalin yankin Checheniya, ya halaka malamin ne a wajen makarantarsa, jim kadan bayan kammala baiwa dalibansa darasi, inda ya nunawa daliban zanen barkwanci na Annabi Muhd Sallallahu Alaihi wa Sallam.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da wasu ke daukar fansa kan cin zarafin da masu zanen barkwanci ke yi wa Musulmi a Faransa ba, ta hanyar batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

A watan Satumban da ya gabata jaridar Cherlie Hebdo ta sake wallafa zanen barkwanci na Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wa Sallam, abinda ya sanya sake kaiwa ofishin jaridar farmaki a birnin Paris inda akalla mutane 4 suka jikkata.

A farkon watan Satumban ne kuma, shugaban Faransa Emmnauel Macron ya yi kakkausar suka kan mutanen da ke neman shaidar zama a kasar amma su ke bijirewa wasu daga cikin dokokinta ciki har da ‘yancin cin zarafi ko batanci da kundin tsarin mulki ya sahale, batun da shugaban ke cewa kowa na da cikakken ‘yancin dariya da caccaka da ma cin zarafi ko tsokana bisa tanadin doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.