Faransa

Sabbin matakan dakile annobar coronavirus za su shafi Faransawa miliyan 20

Birnin Paris
Birnin Paris Gonzalo Fuentes/Reuters

Sabbin matakan dakile annobar coronavirus da ta sake barkewa a Faransa karo na biyu, da suka hada da hana taron jama'a, da kuma fitar dare sun fara aiki a Paris da wasu biranen kasar.

Talla

Matakin hukumomin na Faransa ya zo ne bayan da adadin masu kamuwa da cutar ta coronavirus cikin kasar a rana guda ke cigaba da hauhawa, inda a ranar Alhamis sama da mutane dubu 30 suka harbu da annobar.

Yayin karin bayani kan sabbin matakan yaki da sake yaduwar cutar, firaministan Faransa Jean Castex ya ce daga tsakiyar daren ranar Juma’a gwamnati ta haramta dukkanin tarukan jama’a, zalika za a rika rufe shuganunan saida kayayyaki da sauran wuraren kasuwanci daga karfe 9 na dare zuwa safiya, a dukkanin yankunan da annobar ta Covid-19 ta fi kamari.

Baya ga Paris, sauran biranen da matakan yaki da cutar ta corona suka shafa sun hada da Toulouse, Marseille da kuma Lyon.

A takaice dai matakan hana walwalar za su shafi akalla mutane miliyan 20 daga cikin jumillar miliyan 67 da ke fadin Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.