New Zealand

Yan adawar kasar Neo Zelande sun karba shan kaye a babban zaben kasar

Prayi ministar kasar néo-zélandaise Jacinda Ardern le 17 octobre 2020, à Auckland.
Prayi ministar kasar néo-zélandaise Jacinda Ardern le 17 octobre 2020, à Auckland. AAP Image/David Rowland

Zaben kasar New-zéland: ‘’yan adawa sun amince da nasarar da shugabar gwamnati mai mai ra’ayin kwadago Jacinda Ardern ta samu.Shugabar yan adawar kasar ta néo-zéland uwargida Judith Collins a hukumance, ta tabbatar da nasarar da pm kasar Jacinda Ardern ta samu, a babban zaben kasar da aka gudanar.

Talla

Bayan kammala kirga kashi 2 bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben ne, suka tabbatar da cewa,  pm ta lashe kimanin kujeru 64 cikin 120 da ake da su a majalisar dokoki.

Matar da ta kasance kan mukamin pm kasar ta Neo Zeland tun cikin 2017 Jacinda Ardern, da bata wuce shekaru 40 da haihuwa ba, ta gabatar da yakin neman zabenta ne bisa dogaro da sakamako na gari, da gwamnatinta ta samu musaman ta fannin da yaki da annobar Covid 19.

A lokacin da ta ke tsaokaci kan nasarar uwargida Jacinda Ardern ta godewa daukacin mutanen kasar da suka sake damka amanar tafiyar da mulkin kasar Zeland ga hannunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.