Armenia-Azerbaijan

An cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Armenia da Azerbaijan

Yadda harin makami mai linzami yayi kaca-kaca dawani sashin garin Ganja na kasar Azerbaijan.
Yadda harin makami mai linzami yayi kaca-kaca dawani sashin garin Ganja na kasar Azerbaijan. REUTERS/Umit Bektas

Armenia da Azerbaijan sun cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da ta soma aiki daga daren ranar asabar.

Talla

Kafin cimma yarjejeniyar dai kasashen sun yi ta zargin junansu da karya yarjejeniya ta farko da suka cimma a makon jiya a karkashin jagorancin Rasha, da zumma kawo karshen kazamin yakin da suka shafe sama da makwanni 3 suna gwabzawa kan yankin Nagorno-Karabakh.

Jiya Asabar, Azerbaijan ta ce dakarun Armenia sun halaka mata fararen hula 13, gami da jikkata wasu 50 a harin da ta kai kan garin Ganja, birni na biyu mafi girma a kasar, sai dai Armenia ta ce farmakin martani ne kan makamancinsa da dakarun na Azerbaijan ke ci gaba da kai mata.

Rikicin kasashen dai shi ne mafi muni da aka gani tun bayan yakin da suka gwabza tsakaninsu tsakanin shekarar 1991 zuwa 1994, inda kimanin mutane dubu 30 suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.