'Yan sanda dubu 12 za su tabbatar da dokar hana fitar dare a Faransa
Akalla Faransawa miliyan 20 ne suka yi zaman gidan dole, a daren jiya asabar, sakamakon dokar hana fitar daren da gwamnati ta kafa wasu sassan kasar da annobar coronavirus da ta sake barkewa cikinsu a karo na biyu.
Wallafawa ranar:
Dokar hana fitar daren daga karfe 9, ta soma aiki ne Birnin Paris da kewayensa da kuma wasu manyan biranen guda 8, ciki har da Lyon, Marseille da kuma Saint-Etienne.
Kididdiga ta nuna cewar, kimanin jami’an ‘yan sanda, da Jandarmomi dubu 12 aka girke don tabbatar da aikin dokar.
Yayin da miliyoyin Faransawan suka sake shiga karkashin sabbin matakan hana walwalar, ma’aikatar lafiyar kasar ta ce a jiya asabar din kadai sama da mutane dubu 32 ne gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar ta coronavirus, adadi mafi yawa da aka gani cikin rana guda a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu