Faransa

Faransawa sun yi bore kan fille wuyan wani malami

Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da sara kan Samuel Paty
Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da sara kan Samuel Paty REUTERS/Charles Platiau

Dubban mutane sun fantsama kan titunan a biranen Faransa da suka hada da Paris domin nuna adawarsu da kisan wani malamin makaranta da ya nuna wa dalibansa zanen batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.AW.)

Talla

A birnin Paris, masu zanga-zangar sun hallara ne a dandalin jamhuriya da ake yi wa la’akabi da na ‘yanci, inda da dama ke rike da alluna masu dauke da kalamai daban-daban na nuna goyan bayansu ga malamin mai koyar da tarihi, Samuel Paty da wani matashi mai shekaru 18 dan asalin Checheniya, ya fille wa kai ranar Jumma’ar da ta gabata.

Fraministan Faransa Jean Castex da ya bi sahun masu zanga-zangar, ya wallafa ta shafinsa na Twitta cewar, kisan ba zai razanasu ba, balle raba kawunan ‘yan kasar.

Mista Castex ya samu rakiyar ministan Ilimi, Jean Michel Blanquer da Magajiyar Garin Birnin Paris, Anne Hidalgo da kuma Karamin Ministan Cikin Gida Marlene Schiappa, wadda ta ce ta hallara ne domin nuna goyan bayanta ga malamai da kuma fadin albarkacin baki.

Ko a shekarar 2015, bayan harin da aka kai wa ofishin mujallar Cherlie Hebdo da ta wallafa zanen na batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, sai da Faransawa kimanin miliyan 1.5 suka hallara a wannan Dandali na 'Yanci domin nuna goyan bayansu ga fadin albarkacin baki.

Rahotanni sun ce a biranen Lyon da Toulouse da Strasbourg da Nantes da Marseille da Lille da kuma Bordeaux, duk an gudanar da zanga-zangar goyan bayan malamin da aka fille wa kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.