Faransa

'yan sanda Faransa sun kai samame kan masu goyon bayan jihadi

Ministan cikin gidan Faransa, Gérald Darmanin
Ministan cikin gidan Faransa, Gérald Darmanin Christophe Ena / POOL / AFP

‘Yan sandan Faransa sun kai samame a gidajen dimbin magoya bayan masu ikirarin jihadi a kasar, dake fafutuka ta shafukan sada zumunta, kwanaki uku bayan fille kan wani malamin makaranta da ya nuna wa dalibansa zanen batanci ga manzon tsira annabi Mohammadu (SAW).

Talla

Ministan Cikin Gidan Faransa Gérald Darmanin ya bayyana cewa, matakin na cikin jerin bincike sama da 80 da aka bude, na mutanen da ke goyon bayan kungiyoyi masu ikirarin jihadi da kuma masu kalaman nuna kiyayya ta kafofin sada zumuntan yanar gizo, biyo bayan kisan malamin.

Masu binciken sun fi mayar da hankali ne kan mutanen da suka nuna goyon baya ga matashin mai kimanin shekaru 18 da ake zargi da kisan Samuel Paty, dake koyarwa a wata karamar makarantar sakandaren da aka fille wa kai ranar Juma’a a dai-dai lokacin da yake barin makarantar ​​da ke a wajen birnin Paris.

Ministan na cikin gidan Faransa wanda yace, bazai yi Karin haske ba sai bayan kammala bincike, ya ce tun ranar Lahadi ‘yan sanda sun fara kame, kuma za su ci gaba da haka cikin makon, inda ya kara da cewa kamen da binciken gidajen bai tsaya kan wadanda ake zargi da kisan Paty kawai ba.

‘Yan sandan sun harbe matashin dan yankin Checeniya wanda ake zargi da kisan, jim kadan bayan kashe Malamin.

Yayin da aka tsare da dama daga cikin dangin sa, da kuma mahaifin daya daga cikin daliban Paty wanda ya zargi malamin a yanar gizo da yin batanci ga addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.