Faransa

Faransa ta rufe Masallachin Pantin bayan kisan gillar malamin tarihi

Babban Masallacin birnin Paris.
Babban Masallacin birnin Paris. Zakaria ABDELKAFI / AFP

Hukumomin Faransa sun sanar da shirin rufe Masallachin Pantin dake wajen birnin Paris a wani martani ga masu tsatsauran ra’ayin addinin Islama bayan kisan gillar da aka yiwa wani malamin tarihi Samuel Paty da ake zargi da nuna zanen batunci ga Annabin Rahama.

Talla

Matakin ya biyo bayan binciken da aka gudanar wanda ke nuna cewar wanda ya aikata kisan ya tintibi iyayen wata daliba dake makarantar da Paty ke aiki kafin aikata laifin.

Tuni aka kama mahaifin yarinyar wanda ya kaddamar da shela a Facebook akan malamin ya kuma sanya lambar sa da musayar bayanai da wanda ya aikata kisan kafin lokacin harin.

Daga cikin sakonni da aka gani harda wadanda aka aike ta whatsApp kamar yadda majiyar Yan Sanda ta nuna, kuma cikin su harda faifan bidiyo dake sukar kayan aikin da malamin yayi amfani da su.

Masallachin da aka dauki mataki akan shu ya yada bidiyon a kafar sa ta facebook.

Yan Sanda sun kama mutane 16 da ake zargin suna da hannu cikin aikata kisan, cikin su harda wani da yayi kaurin suna wajen tsatsauran ra’ayi da wasu iyalan gidan Anzorov guda 4.

Ministan cikin gidan Faransa, Gerald Darmanin yace mai tsatsauran ra’ayin da mahaifin dalibar sun gabatar da fatawa akan malamin.

Ministan ilimi Jean-Michel Blanquer yace za’a karrama Paty da lambar girman na kasa da ake kira ‘Legion of Honour’.

Shugaban Masallachin Pantin M’ohammed Henniche yace ya yada bidiyon mahaifin yarinyar ne bai wai domin tantance korafin sa kan zanen da akayi ba, sai dai domin fargabar cewar ana musgunawa yaran Musulmi a cikin aji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI