Turai ta fara daukar sabbin matakan gaggawa kan yaduwar Covid-19

Wasu kasashen nahiyar Turai ciki har da Italiya da Belgium sun dau sabbin matakan gaggawa don dakile sake bullar cutar coronavirus, a yayin da adadin wadanda suka harbu da cutar a duniya ya kai miliyan 40.

Zuwa yanzu fiye da mutum miliyan 40 suka kamu da Coronavirus a sassan Duniya.
Zuwa yanzu fiye da mutum miliyan 40 suka kamu da Coronavirus a sassan Duniya. REUTERS
Talla

Adadin wadanda cutar ta coronavirus ta harba a halin yanzu ya kai miliyan 40, sa’o’i bayan da alkalumman kamfanin dillancin labaran Faransa ya nuna cewa cutar ta lakume sama da rayuka dubu dari 2 da 50.

Gwamnatoci da dama na ta kokarin kaucewa wa kakaba dokar hana zirga zirga kacokan kamar yadda aka gani farkon bullar annobar, don tabbatar da cewa harkokin tattalin arzikinsu ba su tsaya ba.

Amma a wasu kasashen, al’ummomi na adawa da sabbin matakan takaita walwala, da ma sanya mayanin fuska, yayin da ake ta gutsiri tsoma tsakanin gwamnatocin tsakiya da na kananan hukumomi.

A kasar Belgium, wadanda suka kwanta a asibitoci sun ninka da kashi 100 a cikin mako guda kawai, sannan hukumomi sun rufe gidajen sayar da barasa da na abinci tare da kakaba dokar hana fitar dare.

A Italiya, inda cutar ta taba yin kamari a lokacin da ta addabi Turai, gwamnati ce ta sanar da sabbin matakan dakile annoba da suka hada da rufe gidajen barasa da na cin abinci da wuri, sannan ta karfafa batun yin aiki daga gida.

A Australia, sassauta dokar takaita zirga zirga gwamnati ta yi bayan kwananaki 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI