France

Za mu tsaurara matakai a kan masu fakewa da Musulinci don aikata ta'addanci - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. France 2

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar za’a kara kaimi wajen masu fakewa da addinin Islama suna aikata ta’addanci kwanaki 4 bayan kashe wani malami da aka zarga da cin zarafin addinin Islama a kasar.

Talla

Yayin da ya ziyarar da ya kai wajen birnin Paris, shugaban ya ce batun ya wuce na yin maganganu da yawa, sai dai daukar matakan da suka dace kamar yadda al’ummar kasar ke bukata.

Macron ya sha alwashin kawo karshen ayyukan kungiyar dake goyon bayan kungiyar Hamas ta Falasdinawa a cikin kasar saboda samun ta da hannu wajen kashe malamin tarihin da aka yi.

Shugaban ya ce gobe Laraba majalisar ministoci za ta tattauna batun rufe Cibiyar Cheikh Yassine wadda ke goyan bayan yunkurin Falasdinawa da kuma aka sanya sunan wanda ya kafa kungiyar Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.