Ko kun san me yasa Ozil bazai buga wasan Frimiya ba?

Dan wasan Arsenal Mesut Özil.
Dan wasan Arsenal Mesut Özil. REUTERS/Michael Dalder

Masharhanta wasannin kwallon kafa da magoya bayan sun fara hasashe ko tsokaci dangane da makaomar dan wasan Arsenal dan kasar Jamus, Mesut Ozil bayan da aka cire dan wasan mai shekara 32 daga cikin tagawar Arsenal da zasu buga wasannin Firimiya.

Talla

Matakin da ken una cewa dan wasan da ya fi kowa karban albashi mai tsoka na har fam dubu 350 duk mako, bazai bugawa kungiyar wasa ba har sai a watan Fabarairu na badi, idan da hali.

Tsohon dan wasan Arsenal Per Mertesacker ya ce a halin yanzu hankalin Ozil ya fice daga harkokin kwallon kafa, domin kuwa duk da kora da hali da kocin kungiyar Mikel Arteta ke nuna masa, dan wasan ya gommace ya ci gaba da zama koda a benci ne har karshe kwantiragin sa.

Duk da cewa kungiyar na kafa hujja da sharadun kwamitin shirya gasar Firimiya kan batun shekaru da kuma ‘yan kasashen ketare da ya shafi dan wasan aka cire sunansa, amma masu sharhi na ganin rashin bada damar zaftare albashinsa da Orzil ya ki, ya janyo masa kyama a kungiyar.

Yayin da wasu ke alakanta batun da goyan bayan da ya nunawa musulmai ‘yan kabilar Rohinga da ake cin zarafinsu.

Kazalika wasu ke alankanta lamarin da batun auren ‘yar Turkiya da shugaba Erdogan ya yi wakilci.

Mesut Ozil da yakoma Arsenal daga Real Madrid a shekarar 2013, ko ya taka rawar gani wajen taimaka mata samun nasarori.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI