Manchester United ta fara gasar Champions League da kafar dama

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford
Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford Reuters/Carl Recine

Manchester United ta fara wasan gasar zakarun turai na Champions League da kafar dama bayan doke Paris Sait Germent da ci 2-1 a wasan da suka fafata daren jiya duk kuwa da kokarin Neymar da Mbape.

Talla

Marcus Rashford ne dai ya ciwa United kwallon da ya bata damar nasara, bayan da aka kusan tashi wasa 1-1, kuma tarihi ya nuna cewan dan wasan ya taba nuna irin wannan bajinta watanni 18 da suka gabata a filin Parc Des Princes na Farasansar.

United ta fara cin kwallon ta na farko ne ta hanyar fenariti, da aka maimaita sau biyu, bayan da Bruno Fernandes ya buga aka tare, sai dai alkalin wasa ya ce mai tsaron gidan PSG ya kauce layi, Bruno ya sake a karo na biyu ya kuma ci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.