Faransa

Faransa ta karrama malamin da aka fille wa kai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ba za su bada kai bori ya hau ba lokacin da yake jawabin karrama malamin tarihin da aka kashe Samuel Paty, a daidai lokacin da ake gurfanar da wasu dalibai biyu cikin wadanda ke hannu wajen kashe shi saboda yadda suka nuna shi ga wanda ya yi kisan gillar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Lewis Joly / AFP
Talla

Yayin jawabi wajen karrama Paty a Jami’ar Sorbone wanda ya samu halartar iyalan marigayin, shugaba Macron wanda ya ba shi lambar yabo mafi girma ta kasar da ake ba farar hula, ya ce masu tsatsauran ra’ayin addini Islama na neman kwace makomar kasar, kuma ba zasu samu nasara ba.

A waje daya kuma, tuni aka gurfanar da wasu matasa biyu a gaban kotu sakamakon zargin su da ake da nuna Samuel Paty ga makashinsa, wanda ya fille masa kai, inda ake tuhumarsu da hadin baki wajen kisan ta’addanci.

A ranar Laraba, mai gabatar da kara kan laifukn da sukaa shafi ta’addanci Jean-Francois Ricard ya ce matasan biyu masu shekaru 14 da 15 da aka gurfanar na cikin gungun yaran da suka raba kudin da wanda ya aikata kisan ya ba su a matsayin hasafi don su nuna mai Paty.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI