Faransa -Turkiya

Faransa ta janye jakadanta na Turkiya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Lewis Joly / AFP

Faransa ta janye jakandanta daga kasar Turkiyya, tana mai Allah Wadai da kalaman da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi a kan takwaransa na Emmanuel Macron bisa abin da ya kira manufofinsa a kan Musulmai, inda har ma yake cewa Macron na bukatar a duba lafiyar kwakwalwarsa.

Talla

Wani jami’in fadar shugaban Faransa ya bayyana kalaman Erdogan a matsayin abin da ba za su amince da shi ba, inda yake cewa rashin kunya da wuce gona da iri ba hanya ce mai kyau ba, yana mai bukatar Erdogan ya sake fasalin salon diflomasiyarsa saboda wannan na dauke da hadari.

Matakin da Macron ya dauka na kare manufofin kasar na wacce babu ruwanta da harkokin addini daga ayyukan masu tsatsaurar ra’ayin Islama ya harzuka Erdogan, lamarin da ya ta’azzara sabanin da ke tsakaninsu.

A cikin wannan watan ne Macron ya bayyana cewa addinin Musulunci na cikin rikici a fadin duniya, inda yake cewa gwamnatinsa za ta gabatar da wani kudiri da zai karfafa dokar nan ta 1905 da ta rabe tsakanin majami’a da harkokin kasar a hukumance.

Shugaba Erdogan yayi zargin cewar ya dace a duba lafiyar shugaba Macron ne saboda yadda yake musguna wa Musulmi a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI