Wasanni-Kwallon kafa

Real Madrid ta lallasa Barcelona da ci 3-1

Sergio Ramos yana biye da  Lionel Messi a guje a wasan El Clasico da ya wakana a Asabar 24 ga watan Oktoba 2020 à Barcelone.
Sergio Ramos yana biye da Lionel Messi a guje a wasan El Clasico da ya wakana a Asabar 24 ga watan Oktoba 2020 à Barcelone. REUTERS/Albert Gea

Kungiyar Real Madrid ta lallasa Barcelona da ci 3-1 a wasan El Classico na farko a kakar shekarar 2020/2021 da aka buga yau a filin Camp Nou dake Barcelona.

Talla

Valverde ya fara jefa wa Madrid kwallo a mintuna 5 da fara wasan, yayin da Amsu Fati ya farke bayan mintina 3 abinda ya kai ga tafiya hutun rabin lokaci kowacce kungiya na da ci guda-guda.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci alkalin wasa ya bai wa Madrid bugun daga kai sai ma tsaron gida wanda Sergio Ramos ya jefa, yayin da Luka Modric da ya shiga wasan a zagaye na biyu ya jefa kwallo na 3 a minti 90 na wasan.

Wannan nasara ta bai wa Real Madrid damar darewa teburin Laliga da maki 13, yayin da Barcelona ke matsayi na 10 da maki 7 kacal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.