An fara kaurace wa kayayyakin Faransa kan batanci ga musulunci

Wasu kasashen larabawa sun amsa kiran shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da wasu kasashen musulmi wajen soma kauracewa kayakin Faransa, biyo bayan kalaman Shugaban Faransa Emmanuel Macron dake tamkar batanci ga addinin musulunci.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Turkiya Recep Tayyip Erdogan © LUDOVIC MARIN / POOL / AFP
Talla

Shugaban Emmanuel Macron ya bayyana Faransa a matsayin kasar dake kare muradun ta wajen baiwa kowane dan kasar damar fadin albarkacin bakinsa, ta fuskar addini ko al’ada.

Shugaba Macron ya bayyana hakan ne dangane da kisan da aka yiwa mallami tarihin nan, da masu ikirarin jihadi da karfin tsiya suka hallaka kwanakin baya, sakamakon nunawa daliban sa zanen batanci ga manzon tsira Annabi Mohammadu tsiri da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Matakin da ya harzuka wasu kasashen musulmi da yanzu haka suka sanar da dakatar da saya ko amfani da kayakin da aka sarrafa a Faransa ko ke dauke da sunan kasar.

Ranar juma’a 23 ga wannan wata na Oktoba ne kasar Koweit ta shiga sahun gaba daga cikin masu adawa da takawa kayakin Faransa birki a kasarta, lamrain da ya dada yaduwa a sassan wasu kasashen larabawa.

Wasu daga cikin manyan masana’antun Faransa dake sarrafa kayaki da ake shiga da su kasashen Larabawa sun hada da Kiri, da Babybel da suka shafi sashen sufuri sun bayyana damuwa matuka.

Qatar da Koweith da Pakistan na daga cikin jerryn kasashen da suka kauracewa amfani da kayakin Faransa, biyo bayan kalaman Shugaba Emmanuel Macron tun bayan kisan Samuel Patty, sai dai rahotanni daga Masar da Iran da Irak dama Turkiya kamar dai yada wakilan Rfi suka tabbatar ,jama’a basu soma nuna kyamar kayakin Faransa a can ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI