Faransa

Majalisar Kolin Musulmin Faransa ta musanta musgunawa Mambobinta

Wasu Musulmi lokacin da su ke tsaka da Sallah a babban masallachin birnin Nice na Faransa.
Wasu Musulmi lokacin da su ke tsaka da Sallah a babban masallachin birnin Nice na Faransa. Catherine MARCIANO / AFP

Majalisar Kolin Musulmin Faransa ta ce ba a musgunawa Musulmin kasar bayan barkewar takaddama tsakanin masu tsatsauran ra’ayi da ‘yancin fadin albarkacin baki a kasar wanda ya sanya kasashen duniya mayar da martini kan Faransa.

Talla

Sanarwar da Majalisar Musulmin ta gabatar ya bayyana Faransa a matsayin kasaitaciyar kasa wadda bata cin zarafin Musulmi, kuma suna gina Masallatan su da kuma gudanar da ibadun su ba tare da musgunawa ba.

Shugaban Majalisar Mohammed Moussaoui ya bukaci Musulmin kasar da su tashi tsaye wajen kare manufofin su sakamakon korafe korafen dake zuwa daga kasashen duniya.

Moussaoui yace sun san masu yada manufar cewar Faransa na cin zarafin Musulmi na yin haka ne da suna kare Musulmin Faransa, amma suna bukatar su da suyi taka tsan tsan domin kuwa yakin da aka kaddamar kan kasar na iya bata mata suna da haifar da rarrabuwar kawuna.

Dangane da zanen batunci ga addinin Islama kuwa, shugaban yace suma an basu ‘yancin nuna kiyayya akan su.

Yammacin litinin din nan ake saran tawagar shugabannin Majalisar su gana da shugaba Emmanuel Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.