Turai-Covid-19

Spain da Norway sun sa dokar ta baci bayan tsanantar Covid-19 a Turai

Yadda rayuwa ta koma a Madrid babban birnin Spain.
Yadda rayuwa ta koma a Madrid babban birnin Spain. REUTERS/Sergio Perez

Kasashen Turai sun fara bin sahun Spain wajen sanya dokar ta baci don dakile yaduwar cutar Coronavirus, inda a yau Litinin Norway ta sanar tsananta matakan hana walwalar jama'a kwana guda bayan Firaministan Spain Pedro Sanchez ya sanar da dokar ta baci a kasarsa.

Talla

Tun a jiya Lahadi ne Firaministan na Spain Pedro Sanchez yayin jawabin da ya gabatar ta gidan Talabijin ya ce sabuwar dokar tabacin za ta kwashe akalla watanni 6 masu zuwa tana aiki a sassan kasar ko da ya ke bazata shafi Tsibirin Canary ba.

Firaministan na Spain ya bayyana cewa matakin ya zama dole ne la’akari da yadda cutar ke ci gaba da tsananta bayan kamuwar mutane fiye da miliyan guda masu dauke da cutar ta Covid-19.

Da tsakar ranar jiya Lahadi ne mahukuntan kasar da mukarraban gwamnatin Sanchez suka shiga wani tsaron gaggawa na kusan sa’o’i biyu da ya kai ga cimma matsayar ta dokar ta baci da kuma hana zirga-zirgar jama’a daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safiyar kowacce rana.

Kalaman na Firaminista Sanchez ya nuna cewa a karon farko dokar ta cin za ta dauki tsawon kwanaki 15 ne gabanin mikata gaban majalisar dokoki don tsawaita ta zuwa watanni 6 masu zuwa.

Karkashin sabuwar dokar ta bacin yankunan da ke karkashin Spain na da zarafin karawa ko kuma rage lokutan walwalar jama’arsu haka zalika gwamnatin Kasar a shirye ta ke ta wadata su da kayakin agaji idan bukatar hakan ta taso.

A bangare guda, Norway duk da kasancewarta mafi karancin mutanen da ke dauke da cutar a kaf Turai, ta ce daukar matakan takaita walwalar jama'artata ya zama wajibi la'akari da yadda cutar ke yaduwa a nahiyar kamar wutar daji.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI