Turai-Turkiya

EU ta fusata da bukatar Turkiya kan neman a kauracewa kayakin Faransa

Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Olivier Hoslet/Pool via REUTERS

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi ikirarin cewa matakin Turkiya na mika bukatar ganin kasashen Musulmi sun kauracewa sayen kayakin Faransa don mayar da martani ga goyon bayan da Macron ya yi ga zanen batancin da aka yiwa fiyayyen halitta, kai tsaye ya nesanta kasar daga bukatarta ta shirin zama mamba a kungiyar, bukatar da ta mika tun cikin shekarar 1987 amma kuma batun ke tafiyar hawainiya.

Talla

Mai magana da yawun kungiyar Tarayya Turai ya ce, matakin kira
kan kauracewa hajar wata kasa da ke cikin kungiyar EU, ya saba wa
ruhin kungiyar, kuma hakan zai kara nesanta Turkiya daga shiga kungiyar.

Tun a shekarar 1987 Turkiya ta gabatar da kudirinta na shiga
kungiyar tattalin arzikin turai kamar yadda ake kiran EU a wancan
lokaci, yayin da ta fara zaman tattaunawa  a hukumance da EU a shekarar
2005, amma tuni aka dakatar da wannan tattaunawa.

A sabuwar dambarwar da ta barke a tsakaninsu, shugaba Erdogan  ya
bayyana Emmanuel Macron a matsayin mai larurar kwakwalwa, kuma wannan
caccakar na zuwa ne bayan fito-na-fiton da ya wakana tsakanin
shugabannin biyu game da kan iyakar ruwan Turkiya da Girka.

Jirgin ruwan yakin Turkiya ya yi barazana ga jirgin ruwan yakin
Faransa,  yayin da Faransa ta kara kaimi wajen kare Girka kan rikicin
tekun.

Macron dai ya kare ‘yancin demokradiyya da ke bada da damar barkwanci
kan abubuwa da dama da suka hada da addinai, lura da  ikirarin Faransa
na cewa, babu dokar da ke hana barkwanci a kundin tsarin mulkinta.

Wannan ne ya sa ake yin zanen barkwanci kan shugabannin addinai kamar
Fafaroma da malaman Yahudawa.

Sai dai irin wannan barkwancin kan addinin Islama ya kai ga kisan wani
malamin tarihi Samuel Paty a ranar 16 ga watan Oktoba bayan kaddamar
da wani kamfe a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta caccakar malamin
saboda yadda ya nuna wa dalibansa hoton barkwanci da ke batanci ga
addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.