Faransa

Faransa na shirin sake killace al'ummarta saboda korona

Faransa na shirin sake daukar sabbin tsauraran matakan takaita zirga zirga don dakile ta’azzarar cutar Covid -19 da ta sake kunno kai kuma ta buwayi likitoci, inda take nazartar sake daukar matakin killace al’umma a karo na biyu, yayin da asibitoci ke kokarin kula da marasa lafiya da ke kwarorawa.

Wasu daga cikin ma'aikatan dake yaki da Coronavirus a Faransa
Wasu daga cikin ma'aikatan dake yaki da Coronavirus a Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Kwana guda bayan Faransa ta sanar da adadin da ya kai 523 na wadanda cutar coronavirus ta aika barzahun a cikin sa’o’i 24, adadi mafi yawa a rana guda tun a watan Afrilu, shugaba Emmanuel Macron na shirin sanar da karin matakan yaki da wannan cuta zuwa anjima kadan, a jawabin da zai gabatar ga al’ummar kasar.

Manyan jaridu da tashoshin rediyon Faransa sun ruwaito cewa shugaban Macron ya yi amannar cewa akwai bukatar sake killace al’ummar kasar na tsawon makonni 4, batun da ‘yan majalisar dokokin kasar za su kada kuri’a a kai a ranar Alhamis.

Wannan ya sa hannayen jari a kasar sun fadi warwas, inda suka yi kasa da kusan kashi 2 da rabi kafin tsakiyar ranar yau.

Ya zuwa Talata, akwai masu fama da cutar coronavirus kusan dubu 3 a bangaren kwantar da wadanda ke cikin halin rai kwakwai, mutu kwakwai a Faransa, fiye da rabin abin da gadajen asibitoci a bangaren za su iya dauka.

Kusan mutane dubu 19 na kwance gadon asibiti sakamakon harbuwa da wannan cuta, kuma an samu sama da dubu 33 da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI