Amurka-Zabe

Amurkawa da dama ba su gamsu da matakan Trump na yakar Covid 19 ba

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. AP Photo/Ross D. Franklin

A yayin da ya rage saura kwanaki biyar kafin zaben Amurka, ‘yan takaran shugabancin kasar Donald Trump, wanda shine shugaba mai ci da abokin hamayyarsa Joe Biden sun zafafa yakin neman zabe, inda har Biden ya kada kuri’arsa a jiya Laraba, kamar yadda Trump ya yi a makon da ya wuce, a yayin mutane miliyan 74 suka riga suka kada kuri’arsu gabanin zabe.

Talla

Dan takaran jam’iyyar Democrat, Joe Biden ya isa jiharsa, Delaware a ranar Laraba inda ya kada kuri’arsa gabanin zaben shugaban kasar Amurka mai mahimmanci, yana mai ci gaba da nanata yadda yake fatar tinkarar annobar Corona, yayin da Trump ke ci gaba da nuna halin ko in kula.

Yanzu sama da Amurkawa miliyan 74 sun kada kuri’arsu kafin zabe, wanda haka baya rasa nasaba da fargabar shiga hadarin kamuwa da cutar Covid 19 sakamakon cinkoso a zaben Talata mai zuwa, kuma shugaba Trump na magiyar karshe ga masu zabe don su zabe shi a jihohi masu mahimmanci da yake fata ya kame don samun wani wa’adin shekaru 4.

Annobar Coronavirus ta hargitsa dukkan fannoni na rayuwar Amurkawa har ma ta dishe armashin zaben, abin da kuri’a jin ra’ayin jam’a ke nuni da cewa laifin shugaba mai ci ne.

Wani sakamakon kuri’ar jin ra’ayin na cewa, kusan kashi 58 na Amurkawa ba su gamsu da matakan da shugaba Trump ke dauka wajen yaki da Corona ba, yayin kusan kashi 40 na al’ummar suka ce sun gamsu.

Rahotanni daga tawagar yakin neman zaben Biden na cewa tsohon shugaban Amurka, Barack Obama zai hade da tsohon maytaimakin shugaban kasar don neman kuri’un masu zabe a jihar Michigan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.