Jamus

Jamus za ta tallafa wa bangarorin da Covid-19 ta shafa da Yuro biliyan 10

Angela Merkel, shugabar gwamnatin Jamus.
Angela Merkel, shugabar gwamnatin Jamus. John MACDOUGALL / AFP / POOL

Gwamnatin Jamus ta bayyana shirinta na ware Yuro biliyan 10 domin tallafa wa bangarorin da annobar coronavirus ta yi wa illa.

Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jamus ta bada sabon
umarnin rufe wuraren al'adu da na shakatawa har ma da gidajen abinci
domin hana bazuwar cutar coronavirus, yayin da bangarorin da matakin
ya shafa za su ci gajiyar tallafin Euro miliyan 10.

Matakin kullen zai fara aiki ne daga ranar Litinin mai zuwa har zuwa
karshen watan Nuwamba, inda kuma aka takaita taruwar jama'ar da ta
wuce mutun10.

Kazalika an bukaci mutanen kasar da su kaurace wa duk wasu
tafiye-tafiye marasa muhimmanci, yayin da za a bude wuraren kwana
amma ga baki ba 'yan yawon bude ido ba kamar yadda shugabar gwamnatin
kasar Angela Merkel ta fadi bayan ganawarta da shugabannin yankuna 16
na kasar.

Har ila yau za a rufe wuraren shan shayi da gidajen barasa da kuma
gidajen sinima.

Kazalika wuraren wanka da na motsa jiki duk za su kasance a rufe. Amma
za a ci gada da gudanar da wasanni kwallon kafa masu muhimmanci a
bayan fage.

Koda yake makarantu da shaguna za su ci gada da aiki a cewar Merkel.

Sabon matakin na zuwa ne bayan rubanyar adadin mutanen da cutar ta
harba a makon jiya, sannan kuma yawan wadanda ake kwantarwa a sashin
kula da marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali ya k

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.