Faransa

Kasashen Duniya sun yi tir da harin wuka a birnin Nice na Faransa

Shugabannin Kasashen duniya sun yi tir da harin da aka kai Nice da ke Faransa, wanda hukumomi ke gudanar da bincike akai a matsayin harin ta’addanci, inda suka bayyana goyan bayan su ga kasar.

Yankin da aka kaddamar da harin wuka a birnin Nice na Faransa.
Yankin da aka kaddamar da harin wuka a birnin Nice na Faransa. REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Daga cikin wadanda suka bayyana bacin ransu da harin sun hada da shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministan Birtaniya Boris Johnson da Firaministan Italia Giuseppe Conte da shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya da kungiyar kasashen Turai da kuma Fafaroma Francis.

Shugabannin da kungiyar EU sun bayyana damuwa da harin da kuma jajantawa mutanen kasar, yayin Fafaroma Francis ya yi addu’a ga wadanda harin ya ritsa da su, bayan ya bayyana cewar ba za a taba lamuncewa ayyukan ta’addanci da kuma tashin hankali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI