Faransa

Mutane 3 sun mutu bayan wani mutum ya far wa jama'a a Nice na Faransa

Birnin Nice, kusa da Notre-Dame.
Birnin Nice, kusa da Notre-Dame. REUTERS/Eric Gaillard

Wani mutum dauke da sharbebiyar wuka ya kashe mutane 3 bayan da ya kutsa cikin wani coci a birnin Nice na Faransa, kuma daga cikin mutanen da ya kashe, ya yi wa daya yankan rago, kana ya raunata da dama a safiyar Alhamis din nan.

Talla

Masu gabatar da kara kan laifuklan da suka shafi ta’addanci a Faransa sun kaddamar da bincike a kan lamarin da Magajin Garin Nice, Christian Estrosi ya kira harin ta’addanci na masu tsasauran ra’ayin Islama.

Magajin Garin na birnin Nice ya shaida wa manema labarai cewa maharin ya yi ta maimaita kabbara, har zuwa lokacin da ake masa maganin raunukan da ya samu yayin kokarin kama shi.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa, mutane biyun da harin ya rutsa da su sun mutu nan take a majami’ar Basilica ta Notre-Dame, da ke tsakiyar birnin, yayin da mutum na 3 mutu sakamakon raunin da ya ji, bayan da ya nemi mafaka a wata mashaya da ke kusa da inda al’amarin ya auku.

Faransa ta kasance cikin shirin ko ta kwana a kan hare haren ta’addanci tun a shekarar 2015, bayan harin da aka kai wa mujallar barkwanci na Charlie Hebdo biyo bayan batancin da ta yi wa addinin Musulunci.

Yanzu ma haka ana shari’ar wadanda suka kai wannan harin a birnin Paris.

A birnin Nice, har yanzu ba a manta da abin da ya auku a ranar ‘yanci ta Bastille, inda wani mutum ya zaburar da wata katuwar mota cikin taron jama’a, ya kashe mutane 86 aranar 14 ga watan Yuli ta shekarar 2016.

Wannan hari na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da dubban al’umma suka yi wani gangami na nuna goyon baya da alhini ga wani malamin tarihi da aka fille wa kai bayan da ya nuna wa dalibansa zanen barkwanci da aka yi na Annabi Mohammed (SAW).

Wani dan kasar Chechniya mai shekaru 18, Abdullahk Anzorov ne ya kashe malamin tarihin, Samuel Paty.

Kisan malamin ya janyo dirar mikiya a kan masu tsatsauran ra’ayin Musulunci daga shugaban Faransa Emmanuel Macron, ciki har da matakin rufe masallatai da kungiyoyi da ake zargi da goyon bayan ta’addanci.

Sai dai matakin na Macron ya harzuka kasashen Musulmai da dama, inda wasu ke zarginsa da muzgunawa Musulmai kusan miliyan 6 da ke Faransa.

An yi ta zanga zanga a wasu kasashen Musulmai har da kaurace wa kayayyakin da suka fito daga Faransa, kana zaman tankiya ya kunno kai tsakanin Macron da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.