Turkiya

An zakulo dattijo da rai a baraguzan gini bayan sa'o'i 34 da girgizar kasar Turkiya

Ma'aikatar shari'ar Turkiya ta nemi gudanar da bincike don gano ko akwai sakaci daga jami’an gwamnati.
Ma'aikatar shari'ar Turkiya ta nemi gudanar da bincike don gano ko akwai sakaci daga jami’an gwamnati. IHA via AP

Masu aikin agaji a Turkiya sun yi nasarar zakulo wani dattijo mai shekaru 70 a karkashin buraguzan ginin da ya rushe ranar juma’a bayan sa’o'i 34 da girgizar kasar da aka samu a kasar wadda ta kashe mutane akalla 60 yanzu haka.

Talla

An dai zakulo Ahmet Citim ne daren jiya kuma nan ta ke aka ruga da shi zuwa asibiti inda ake kula da lafiyar sa, kamar yadda ministan lafiya Fahrettin Koca ya bayyana bayan ya ziyarce shi a asibiti.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan yau ya bayyana cewar mutane 58 suka mutu a Izimir sakamakon girgizar kasar, yayin da aka bayyana rasuwar wasu kananan yara guda 2 a Samos, kana wasu 19 sun samu raunuka.

Mataimakin shugaban kasa Fuat Oktay ya ce za a rusa gine-gine 26 da suka samu matsala sakamakon karfin girgizar kasar ya lalata su.

Rahotanni sun ce daga cikin benayen da suka rushe akwai wasu guda biyu da bincike ya nuna cewar sun lalace tun daga shekarar 2012 da 2018.

Ministan shari’a ya ce tuni masu bincike suka fara aikin su domin gano ko akwai sakaci daga jami’an gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.