Bisa dukkan alamu dai an kamala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba don babban zaben kasar Amurka a gobe Talata tsakanin shugaba mai ci Donald Trump na Jamiyar Republican da kuma Joe Biden na Jamiyar Democrat.Ganin yadda duniya ta zaku a ga yadda zaben zai kaya mun tuntubi Abdulrahman Dandi Abarshi dan kasar Niger mazaunin Indian na Amurkan ko wani shiri aka yin a wannan zabe.
Sauran kashi-kashi
-
Bakonmu a Yau Sabuwar gwamnatin Katsina ta sha alwashin magance matsalar tsaro Sabuwar gwamnatin jihar Katsina ta Najeriya da ta yi rantsuwar kama-aiki a wannan Litinin ta bayyana sabbin matakan da za ta dauka wajen magance matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare durkusar da tattalin arzikinta.29/05/2023 03:22
-
Bakonmu a Yau Farfesa Usman Muhammad kan bikin rantsar da sabon shugaban Najeriya A ranar 29 ga watan Mayun 2023, aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya domin maye gurbin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda ya kawo karshen wa’adin mulkinsa na shekaru 8.29/05/2023 03:38
-
Bakonmu a Yau Zainab Ahmed kan basussukan da ake bin Najeriya Yayin da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kawo karshen wa’adin ta a ranar litinin mai zuwa, daya daga cikin zargin da ake mata shine na ciwo basussuka daga hukumomin duniya, wadanda suka yiwa kasar dabaibayi.26/05/2023 03:45
-
Bakonmu a Yau Kungiyar tarayyar Afrika ta cika shekaru 60 ga kafuwa kungiyar tarayyar Afrika ta cika shekaru 60 da kafuwa a dai dai wannan lokaci da nahiyar ke fuskantar matsaloli da kalubale kala kala musaman ma na tsaro fadace fadace tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyin yan tawaye, ko kuma da kungiyoyin dake ikrarin jihadi, da kuma na yan bindiga.To domin jin irin nasarorin da aka samu a cikin wadannan shekaru, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Bako masanin siyasar duniya a jami'ar Bayaro dake Kano Najeriya.25/05/2023 03:42
-
Bakonmu a Yau Birtaniya na shirin takaita baiwa dalibai yan kasshen ketare Biza Gwamnatin Birtaniya ta takaita adadin takardun bizar da take bai wa dalibai ‘yan kasashen waje da ke karatu a kasar, biyo bayan hauhawar adadin bakin da ke shiga cikin Birtaniyar da sunan iyali ko ‘yan uwan daliban.24/05/2023 03:35