Faransa

'Yan sandan Faransa suna tsare da wasu mutane dangane da harin Nice

Wasu majiyoyi da ke sa ido a binciken da ake kan hare haren da aka kai kasar Faransa a kwanan nan sun ce ana tsare da wani mutum da aka yi amannar shi ya yi balaguro don cin rani daga Tunisia tare da matashin da ya kai harin wuka a birnin Nice, a daidai lokacin da Kiristoci mabiya mazabahar Katolika ke kokarin cire tsoron halartar sujjada a majami’u daga zukatansu.

Jami'an tsaro a harabar ikilisiyar Basilique Notre Dame jim kadan bayan harin da wani ya kai cocin da wuka..
Jami'an tsaro a harabar ikilisiyar Basilique Notre Dame jim kadan bayan harin da wani ya kai cocin da wuka.. REUTERS/Eric Gaillard/Pool
Talla

Mutane 3 ne suka mutu a harin da aka kai da wuka a majami’ar Basilica ta Notre-Dame a ranar Alhamis, harin da aka ce wani matashi da ya isa Turai daga Tunisia babu dadewa ya kai.

Wannan ne hari na baya bayan nan da da aka kai Faransa, wanda gwamnatin kasar ta bayyana a matsayin harin ta’addanci na masu tsatsauran ra’ayin Islama, jim kadan bayan sake wallafa zanen barkawancin da ya yi batanci ga annabi Mohammed (SAW) da mujallar Charlie Hebdo ta yi a watan Satumba.

A birnin Nice, ‘yan sanda sun saki wasu mutane 3 da aka tsare bayan da hukumomi suka tabbatar da cewa babu wani abi da ya hada su da wanda ake zargi da kai harin, Brahim Issaoui, a cewar majiyoyn.

Wasu karin mutane 3 kuwa, ciki har da wani mutum mai shekaru 29 dan kasar Tunisia da ake zargin shi ya kawo Issaoui Turai suna hannun hukuma.

Issaoui mai shekaru 21, ya sauka a tashar jiragen ruwan Italiya ta Bari ne a ranar 9 ga watan Oktoba, kafin ya nufi birnin Nice kwanaki 2 kafin aikata aika aikar da ake zarginsa da aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI