Turkiya

Adadin mutanen da girgizar kasa ta kashe a Turkiya ya kai 100

Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar Turkiya ya karu zuwa mutum 100 yau Talata inda ake da jumullar mutum 994 da suka jikkata a ibtila’in.

Kawo yanzu ana ci gaba da aikin zakulo mutanen da suka bace a baraguzan gine-gine.
Kawo yanzu ana ci gaba da aikin zakulo mutanen da suka bace a baraguzan gine-gine. SHKULLAKU / AFP
Talla

Sanarwar da hukumar kula bal’o’i ta Turkiya ta fitar ta ce girgizar kasar mai karfin maki 7 da ta dirarwa kasar cikin makwan jiya ta yi mummunar barna inda kawo yanzu ake ci gaba da laluben wadanda suka bace a baraguzan gine-gine.

Acewar hukumar yanzu haka akwai jumullar mutum 147 da ke karbar kulawa a Asibitoci yayinda ake ci gaba da zakulo wasu da sauran ransu a karkashin gine-ginen da suka zube.

Yanzuy haka dai a yankin Izmir da ibti la’in ya fi tsananta ana ci gaba da aikin ceto bayan nasarar zakulo yarinya mai shekaru 3 da ranta duk da shafe kwanaki 3 a karkashin gine-gine ko da ya ke dan uwanta da ginin ya bunne su tare ya rasa ransa lokaci kankani bayan fito dashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI