Amurka

Ana tafiya kankankan tsakanin Trump da Biden a Florida

Wasu Amurkawa yayin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa
Wasu Amurkawa yayin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa Reuters

Bayanan da suka soma fita dangane da sakamakon kuri’un da aka a zaben shugabancin Amurka sun nuna cewa ana tafiya kankankan a jihar Florida tsakanin shugaba mai ci Donald Trump na jam’iyyar Republican da abokin hamayyarsa Joe Biden na Democrats.

Talla

Sai dai masu sharhi sun yi gargadin yayi wuri a tantance dan takarar da zai nasarar lashe mafi rinjayen kuri’u a jihar ta Florida.

Duk wanda ya samu nasarar lashe zaben a jihar Florida tsakanin Trump da Biden, ya kama hanyar samun mafi rinjayen kuri’un wakilan musamman na kwamitin zaben shugaban kasadaadadin 270 daga cikin 538, wadanda ke yanke hukuncin karshe a zaben na Amurka.

Zuwa lokacin wannan wallafa rahotanni sun ce an kidaya sama da kashi 90 na kuri’un zaben shugabancin Amurkan da aka kada a jihar Florida.

A bangaren kuri’un wakilan kwamitin zaben shugaban kasa kuwa, sakamakon da ya soma fitowa ya nuna dan takarar jam'iyyar Democrats Joe Biden ke kan gaba da adadin kuri'u 131, yayin da shugaba Donald Trump ke kuri'u 92.

Dan takara dai na bukatar samun kuri’u 270 a tsakanin wakilan na musamman a kwamitin yanke hukuncin karshe kan zaben shugabancin Amurka, kafin samun nasarar zama shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.