Amurka

Bai kamata Amurkawa su jira sakamakon zabe ba-Trump

Shugaban Amurka Donald Trump yace Amurkawa suna da hurumin sanin wanda suka zaba shugaban kasa a ranar da aka gudanar da zabe, sabanin yadda sakamakon ke wucewa rana ta biyu a wasu lokuta.

Shugaban Amurka Donald Trump yayin yaken neman zabe a jihar Michigan
Shugaban Amurka Donald Trump yayin yaken neman zabe a jihar Michigan AP Photo/Evan Vucci
Talla

Yayin da yake tsokaci kan zaben na yau, Trump yace ba daidai bane a bar Amurkawa suna ta jira, yayin da a wasu jihohi ana cigaba da kirga kuri’u har zuwa rana ta 3 duk da amincewar kotun koli.

Kididdigar kuri’un wuri da Amurkawa suka kada kafin ranar zabe ta nuna cewar adadin ya kusan miliyan 102, kwatankwacin kasha 73 na jumillar yawan wadanda suka kada kuri’unsu a zaben shugabancin Amurka na shekarar 2016.

Zaben wuri, ko kada kuri’u kafin ranar zabe ta hanyoyin akwatunan gidan waya ko kuma zuwa kafa da kafa ya samu karin karbuwa a Amurka ne saboda annobar coronavirus da ta halaka sama da mutane dubu 220 a kasar. Hakan ta sanya don kaucewa kamuwa da cutar miliyoyin Amurka suka zabi jefa kuri’unsu kafin ranar zabe.

Ana sa ran fuskantar tsaiko dangane da kamala kidayar kuri’un da aka kada ta hanyar akwatunan gidan waya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI