Amurka

Tasirin da annobar Coronavirus ta yi kan zaben Amurka

Miliyoyin Amurkawa sun soma jiran sakamakon kididdigar kuri'unsu da suka kada don zaben ko dai shugaba mai ci Donald Trump kan wa'adi na biyu, ko kuma dan takarar Democrats Joe Biden.
Miliyoyin Amurkawa sun soma jiran sakamakon kididdigar kuri'unsu da suka kada don zaben ko dai shugaba mai ci Donald Trump kan wa'adi na biyu, ko kuma dan takarar Democrats Joe Biden. AFP

Cikin watan Fabarairun wannan shekara ta 2020, mafi akasarin masu sharhi kan siyasar Amurka sun cimma matsayar shugaba mai ci Donald Trump na da kyakkyawar dama ta sake lashe zaben shugabancin kasar karo na biyu cikin sauki.

Talla

Masu sharhin kuwa sun kafa ginshikin hasashensu ne kan wasu muhimman batutuwa da suka hada da karuwar karfin tattalin arzikin Amurka a karkashin gwamnatin Trump a dalilin manufofin fifita Amurkan a ciki da wajen kasar, da kuma kasancewarsa shugaba mai ci.

Sai dai cikin bazata lamurra suka sauya, sakamakon barkewar annobar coronavirus, da ta zama ‘ruwan dare game duniya’, zalika a lokaci guda annobar ta zama madubin da Amurkawa gami da sauran kwararru ke tantance salo da manufofin yakin neman zaben shugaba Donald Trump na jam’iyyar Republican da kuma abokin hamayyarsa Joe Biden na jam’iyyar Democrats, wanda a baya ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar ta Amurka a gwamnatin tsohon shugaba Barrack Obama.

Salon da ‘yan takarar biyu ke amfani da shi wajen tunkarar annobar ta coronavirus ya taka muhimmiyar rawa wajen kara raba kawunan Amurkawa da kuma haifar da sauyi ga shekarar da zaben shugabancin kasar ta Amurka ke gudana.

Dan takarar jam’iyyar adawa ta Democrats Joe Biden ya maida annobar ta coronavirus da yadda shugaba Trump ke tunkararta muhimman batutuwa a yakin neman zabensa, inda ya rika yawaita tunasar da Amurkawa yawan mutanen da cutar coronavirus ta halaka a kasar da adadinsu ya zarta dubu 227, 000.

A nashi bangaren shugaba Trump ya cigaba da nanata cewar yayi namijin kokari wajen dakile annobar ta coronavirus da yayi ikirarin ba don matakan da gwamnatinsa ta dauka ba, da miliyoyin Amurkawa ne za su rasa rayukansu.

A cewar Trump, shirinsa na farfado da tattalin arzikin Amurka, da tashi tsaye kan ganin an samar da alluran rigakafi ko maganin annobar coronavirus sun isa nuna cewar ya cancanci yabo da kuma sake bashi damar zarcewa bisa shugabanci wa’adi na 2.

Cikin watan Oktoban da ya gabata ne kuma shugaba Trump ya kamu da cutar ta Coronavirus, tare da wasu ma’aikatan fadar White House da na yakin neman zabensa da dama da suma gwaji ya nuna sun kamu da cutar.

Tasirin Coronavirus kan tsarin zaben Amurka

Tasirin wannan annobar dai ya haifar da sauyi ga zaben Amurka ta hanyar tilastawa hukumomin zabe a matakan jihohi da kananan hukumomi rungumar tsarin kada kuri’a ta akwatin gidan waya, da kuma karfafawa Amurkawa gwiwar kada kuri’unsu da wuri kafin ranar zabe, wato 3 ga watan Nuwamban da muke ciki, ko dai ta hanyar akwatin na gidan waya, ko kuma ta hanyar zuwa rumfunan zabe kafa da kafa.

Kididdiga ta nuna cewar kafin ranar zabe sama da Amurkawa miliyan 80 ne suka kada kuri’unsu ta hanyar akwatunan gidan waya ko kuma yin tattaki zuwa rumfunan zabe, adadin da ya zarta kuri’un wuri miliyan 57 da Amurkawan suka kada a zaben shugabancin kasar na shekarar 2016.

Annobar Coronavirus ta sauya salon yakin neman zabe a Amurka

Da fari dai annobar coronavirus ta dakatar da tarukan yakin neman zabe na tsawon wani lokaci, sai dai daga bisani shugaba Donald Trump ya cigaba da gangamin yakin neman zabensa dake tara dubban jama’a a jihar Oklahoma.

Trump ya maida hankali wajen yakin neman zaben ne bayan warkewa daga cutar coronavirus da ya harbu da ita, wadda ta tilasta masa kauracewa shiga jama’a na tsawon kwanaki 10.

Tarukan siyasar Trump dai sun rika gudana ne ba tare da kiyaye sharuddan neman kariya daga annobar ba, inda mafi akasarin dubban mutanen dake halartar gangamin yakin neman zaben basa sanya takunkuman rufe baki da hanci, da kuma kiyaye baiwa juna tazara.

Sai dai dan takarar jam’iyyar Democrats Joe Biden salon takaita shirya gangamin yakin neman zabensa ya runguma, zalika a duk lokacin da ya halarci tarukan jama’ar anan kokarin kiyaye baiwa juna tazara don dakile annobar coronavirus.

A lokuta da dama tarukan gangamin siyasar Joe Biden sun gudana ne a wuraren ajiya motoci, inda magoya bayansa ke sauraron jawabinsa daga cikin motocinsu.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka wallafa ya nuna cewar kashi 40.6 na Amurkawa sun gamsu da matakan dakile annobar coronavirus da shugaba Donald Trump ke dauka, yayinda kashi 56.6 suka nuna rashin gamsuwa da salonsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.