Faransa-Macron

Faransa na yaki ne da tsattsauran ra'ayi ba addinin Islama ba- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Photo by Ludovic Marin, Pool via AP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasar sa na yaki ne da tsatsauran ra’ayi amma ba addinin Musulunci ba a wata wasikar korafi da ya aikewa Jaridar Financial Times da ya zarge ta da sauya kalaman sa, wanda tuni ta cire a shafukanta.

Talla

A wasikar da ya rubutawa Editan Jaridar kuma aka wallafa jiya laraba, Macron ya zargi jaridar ta Birtaniya da zargin sa da shafawa Musulmin Faransa kashin kaji saboda bukatar sa ta zabe da kuma jefa shakku da tsoro a tsakanin su.

Macron ya ce bai zai taba yarda wani ya yi zargin cewar Faransa ko gwamnatinta na nuna wariya ga al’ummar Musulmi ba, sabanin matsayin wakilin Jaridar cewar sukar da shugaban ya yi wa addinin zai jefa karin tsana akan Musulmin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.