Macron ya rusa tare da haramta kungiyar masu kishin Turkiya a Faransa
Gwamnatin Faransa ta ce, ta rusa Kungiyar Grey Wolves, kwanaki biyu bayan ta sanar da haramta kungiyar ta masu tsananin kishin kasar Turkiya, dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin shugaban kasar Emmanuel Macron da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyan.
Wallafawa ranar:
Majalisar Ministocin Faransa ce ta dauki matakin rusa kungiyar ta Grey Wolves bayan wasu zane-zane da aka yi a cibiyar tunawa da Armeniyawan da aka yi wa kisan kare dangi a lokacin yakin duniya na 1.
Ministan Cikin Gidan Faransa, Gerald Darmain ya ce, Kungiyar na haifar da matsalar nuna wariya da kiyayya, sannan kuma tana da hannu a tashe-tashen hankula a cewarsa.
Ana kallon wannan Kungiya ta Grey Wolves a matsayin wani reshe na Jam’iyyar da ke kawance da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan wanda a ‘yan kwanakin nan ya ke takun saka da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.
Rusa wannan kungiya na zuwa ne a daidai lokacin da tashe-tashen hankula suka tsananta tsakanin al’umomin Turkiya da Armeniya mazauna Faransa.
Turkiya ta goyi bayan aminiyarta Azerbaijan a ricikin yankin Nagorno-Karabakh wanda ke karkashin ikon ‘yan awaren Armeniya tun tsakankanin shekarun 1990.
Ko a makon jiya, sai da mutane hudu suka jikkata a birnin Lyon na Faransa a wata arangama tsakanin maambobin kimgiyar ta Grey Wolves da Armeniyawa da ke zanga-zangar nuna adawa da yadda Azerbaijan ke kai harin soji a
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu