Biden ya sha alwashin tinkarar annobar Corona a ranar farko
A yayin da yake daf da lashe zaben shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya sha alwashin tinkarar yaki da annobar coronavirus ba tare da bata lokaci ba da zarar ya dare madafun iko.
Wallafawa ranar:
A jawabin da ya gabatar a Juma’ar nan, Biden ya bayyana kwarin gwiwar dada shugaba Donald Trump da kasa, a yayin da ake ci gaba da kidaya kuri’un da Amurkawa suka kada tun a ranar Talata da ta gabata.
Biden ya sha alwashin hada kan al’ummar kasar, yana mai kira a garesu da su hada kai a matsayinsu na kasa don samun waraka.
Ba a kai ga bayyana wanda ya lashe wannan zabe na shugaban kasar Amurka ba, amma Biden ya sha alwashin soma tinkarar matsalar annobar coronavirus da zarar ya hau kujerar shugabancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu