Iran na fatar ganin sabuwar gwamnatin Amurka ta koyi darasi

Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani ya bukaci ganin sabuwar gwamnatin kasar mai zuwa za ta koyi darasin cewar takunkumi ba zai taba sanya kasar ta sauya manufofin ta ba.

Shugaban Iran Hassan Rohani.
Shugaban Iran Hassan Rohani. © AFP
Talla

A jawabin da ya yi wa al’ummar kasar, Rouhani ya bayyana cewar darussan da aka gani a cikin shekaru 3 da rabi na mulkin shugaba Donald Trump zai taimaka wa Amurka wajen shiga taitayinta na aiki da dokokin duniya da kuma mutunta alkawarin da ta yi.

Shugaban ya ce mutanen Iran sun gamu da ta’addanci kan tattalin arzikin su na shekaru 3 da suka gabata, kuma kasar za ta cigaba da kare manufofinta da kuma nuna hakuri har sai Amurkar ta mutunta dokokin duniya.

Rouhani ya ce bukatarsu ita ce kasashen dake sanya takunkumi su fahimci cewar hanyar da suka dauka ba mai bullewa bace, kuma zata biya musu bukata ba.

Kasar ta Iran na fatar ganin nasarar jam’iyyar Democrat zata bada damar mayar da Amurka cikin yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla da ita, duk da yake shugaban addinin Iran Ayatullah Ali Khamenei ya ce basu da yakinin cewar manufofin Amurkar na iya sauyawa idan an kawar da Trump daga karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI