Amurka-Biden

Zan maido da kimar Amurka a idon duniya - Biden

Dan takaran jam’iyyar Democrat, Joe Biden kuma zababben shugaban Amurka da ya kada shugaba mai ci Donald Trump, ya sha alwashin kawo hadin kai a kasar, a jawabinsa na farko tun da ya samu wannan nasarar mai dimbim tarihi.

Joe Biden, zababben shugaban Amurka.
Joe Biden, zababben shugaban Amurka. AP Photo / Andrew Harnik
Talla

Biden ya gabatar da wannan jawabi ne a mahaifarsa ta Wilmington a gaban dimbim magoya bayansa, ga kadan daga abin da ya ke cewa.

Jawabin nasarar da Biden ya gabatar ya biyo bayan gwabzawa mai zafi da suka yi da shugaban Amurka mai ci, Donald Trump a takarar shugabancin kasar, a daidai lokacin da annobar coronavirus ke ta’azzara a kasar.

Biden wanda ya yi alkawarin kawo hadin kai a kasar ya yi kira ga, magoya bayan Trump da su kwantar da hankulansu, don su ba abokan gaba bane, ‘yan Amurka ne su.

Daga nan sai ya sha alwashin maido da kimar Amurka a idon duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI