Amurka

Biden zai kaddamar da tawagar da za ta kawar da Coronavirus daga Amurka

Yau litinin ake sa ran zababben shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana tawagar kwararrun da zai kafa don yakar annobar coronavirus a Amurka d zarar ya kama aiki.

Zababben shugaban Amurka Joe Biden
Zababben shugaban Amurka Joe Biden AP Photo/Andrew Harnik
Talla

Dakon kafuwar wannan tawaga na zuwa ne a daidai lokacin da adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya ya haura miliyan 50.

Tun a jawabinsa na farko bayan samun nasarar zama zababben shugaban Amurka, Joe Biden ya yi alkawarin kafa tawagar kwararrun kan sha’anin lafiya da zummar kawo karshen annobar coronavirus a kasar, abinda yace zai fi baiwa fifiko da zarar an rantsar da shi, a ranar 20 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2021.

Kawo yanzu annobar ta coronavirus ta halaka sama damutane dubu 237 a Amurka, kuma tana cigaba da yaduwa a sassan kasar.

Sabbin alkaluman da kwararrun jami’ar John Hopkins suka fitar kan annobar sun nuna cewar adadin wadanda suka kamu da cutar a Amurka na gaf da kaiwa miliyan 10, kuma babu alamun za ta sassauta a nan kusa, duk da cewa shugaba mai barin gado Donald Trump ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa na gaf da dakile annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI