EU-Amurka

Lokaci ya yi da EU za ta daina dogaro da Amurka - Kwararru

Tutar kungiyar Tarayyar Turai.
Tutar kungiyar Tarayyar Turai. Reuters/file photo

Kungiyar kasashen Turai za ta sake kulla sabuwar hulda da Amurka a karkashin mulkin zababben shugaban kasar, Joe Biden.

Talla

Sai dai masu sharhi sun gargadi EU dangane da dogaro da Amurka wajen bada kariya ga Kasashen NATO.

A yayin aika wa Joe Biden sakon taya shi murnar lashe zaben Amurka, babban jami’in diflomasiyar Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrel ya bayyana fatar cewa, EU da Amurka za su dinke domin gudanar da aiki tare.

Sai dai tsohon shugaban Hukumar EU, Jean Claude Juncker ya yi kakkausar magana, yana mai cewa Biden ba zai iya sauya lamurran da suka shafi Amurka da kasashen duniya cikin dare daya ba.

Kazalika shugaban Cibiyar Jacques Delors, And Sebastian Millard, ya ce, ya zama wajibi kasashen Turai su koyi yadda za su rika rayuwa ba tare da jagorancin Amurka ba.

Shi ma wani fitaccen masanin kimiyar siyasa a Jamus, Markus Kaim, ya bayyana cewa, nan gaba kadan, AMurka za ta ci gaba da fama da kanta ne,a don haka, dole EU ta fara koyan yadda za ta yi raywa ita kadai.

Kodaya ke Juncker ya ce, al’amura za su yi sauki karkashin mulkin Joe Biden lura da cewa ya fi Donald Trump fahimtar alkibilar kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.